The Universal Church celebrates Mission Sunday today

The universal church today celebrates the Mission. below is message of Pope Francis for World Mission Day 2016.

Hausa Translation

SAKON PAPA ROMA FRANCIS NA RANAN YADA BISHARA 2016

Ikkilisiya mai yada Bishara, Shaidar Jinkai

Yan'uwa Kaunatattu,

Shekara ta musanman na babbar buki na Jinkaì, wadda Ikkilisiya take ciki, ya kara bada haske na musanman a kan Lahadi ta Yada Bishara 2016: gayyata ce gare mu yadda zamu dubi aikin yada bishara a kan aiki ne na jinkai a cikin ruhaniya da ta jiki. A wannan Lahadi ta yada Bishara, an gayyace mu duka “mu fita” kamar almajirai na yada Bishara, kowa yana bada basirarsa, iya haifar da sabon abu, hikima da kuma sanin abubuwa domin kawo sakon Allah cike da tausayi ma dukan iyali ta bil’adama. bisa ga-imanin wannan umurni na yada bishara, Ikkilisiya tana kula da wadanda basu san Bishara ba, domin burin ta shi ne kowa ya sami ceto ya kuma ji yadda kaunar Ubangiji take. An kaddamar da Ikkilisiya ta yi shelar Jinkai na Allah, wadda ita ce bugun zuciyar Bishara" (Misericordiae Vultus 12) ta kuma sa kowace kusurwa ta duniya ta ji shelar Jinkai ga kowa daga matasa zuwa tsofaffi.

Idan jinkai ta sadu da mutum takan kawo murna sosai cikin zuciyar Allah Uha; gama tun da farko Allah Uba cikin kaunarsa yana fuskantar marasa karfi domin girma da ikonsa suna bayyana ne sa'alin da yake nuna kansa tare da matasa, wadanada aka yashe su, da wadanda ake toshe hakkìnsu (Duba Kubawar Shari'a 4:31; Zabura 86:15; 103:8: 111:4), Shi Allah ne mai tausayi, mai kula da kuma mai aminci wanda yake kusa da masu bukata, musanman talakawa; kamar yadda uba da uwa ke sa Kansu cikin rayuwar ya’yansu haka Allah Uba yakan sa kansa cikin rayuwar yan adam(Duba Irmiya 31:20). Littafi Mai Tsarki ta yi amfani da Kalmar mahaifa domin ta alamce jinkai; wato mahaifa ta nuna irin kaunar da uwa take da shi ma ya’yan ta wanda a kowace hali da duk abin da xai faru zata kaunace su kowane lokaci domin su daga mahaifanta ne. Itin wannan kauna ce muhinmin yanayin kaunar Allah ga ya’yansa wadanda ya halite yana kuma so ya yi renon su ya illimmantad da su. Tausayi da rahama takan mamaye zuciyarsa Idan ya fuskanci kasawa da rashin amincin su (Duba Yusha'u 11:8). Yana nuna Jinkai wa kowa; kaunarsa wa kowa ne rahamarsa kuma ta shafi dukan hallita (Duba Zabura 144:8-9).

Ta wurin Kalma da ya zama mutum ne Jinkai take samun darajarta da cikakkiyar bayyanuwar ta. Yesu ya nuna fuskar Uba mai arzikin jinkai; “ta yin amfani da kwatantawa da kalmomi a dunkule ya yi Magana a kan jinkai ya kuma bada bayani.” (Yahaya Bulus II, Dives in Misericordia, 2). Idan ta wurin Bishara da Sakramenti mun marabce mun kuma bi Yesu, tare da taimakon Ruhu Mai Tsarki zamu iya zama masu jinkai kamar yadda Ubanmu na sama yake da jinkai; muna iya koyi da irin kaunar da yayi mana wadda ta kaunarsa ya bamu kyautar rayukanmu, alamar alherinsa (Duba Misericordiae Vultus, 3). A cikin bil'adama, Ikkilisiya a farko ita ce muhalli da ke rayuwar ta bisa ga jinkan Kiristi: takan ji yadda yake duban ta kuma ta ji yadda ya zabe ta domin kaunarsa mai jinkai. Ta wurin wannan kauna ne Ikkilisiya takan tsinci ta kuma gane umarnin ta na yin bishara, tana rayuwar bisharan ta kuma sa dukan mutane su sami sanin bisharan ta wurin hulda cikin bangirma wa kowaco ol'ada da addini.

A wurare da dama, aikin bishara takan fara da ilimantarwa wanda akan bada lokaci sosai da kuma kwazo kamar yadda mai kula da gonar inabi cikin Bishara ke yi (Duba Lk 13:7-9; Jn 15:1 ), da hakuri zai jira ya'ya bayan shekarun noma cikin lura; ta wannan hanya sukan haifar da sabbin masu aikin bishara, wadanda zasu kai bishara a wuraren da ba'a zata bishara zata kai ba. Ana iya bada ma'anar Ikkilisya a kan ita “UWA” ce ga wadanda wata rana zasu sami kyautar bangaskiya cikin Kiristi. Bege na kuwa ita ce jama'ar Allah masu tsarki su ci gaba da wannan bauta na jinkai irin ta uwa, wanda zai taimaki wadanda basu san Ubangiji ba su sadu da shi su kuma kaunace shi. Bangaskiya muhimmiyar kyautar Allah ce ba sanadiyyar jawo mutane ga sabuwar addini ba. BangaskiyaWannan kauna mai jinkai ne tun kwanaki na farko na Ikkilisiya mutane da yawa maza da mata daga kowane wuri cikin kowane hali sun bada shaidar sa, Yadda ake samun kasancewar mata a aikin yada Bishara tare da abokan aikinsu maza, alama ce ta kaunar Allah irin ta Uwa. Akwai hanyoyi da dama wanda wasu mata, sistoci da wadanda suke jama'ar Allah, har ma iyalai da dama suke aiwatar da kiransu ga aikin bishara: daga yin shelar bishara zuwa aikin agaji na bauta. Ta hada hannu da ma'aikatan yada bishara cikin aikinsu na bada sakramenti da bishara, wasu mata da kuma iyalai sukan fi gane damuwoyin mutane da yadda za'a magance su ta mafificin hanyoyi: suna kula da rayyuka da niyya sosai wajen gina mutane fiye da gina abubuwa, suna kuma yin amfani da abin da suke da shi ta fallin ruhaniya da jiki su gina dangantaka masu armashi, zumunci, salama, taimakon juna, hulda, hada hannu da kuma zumuncin yan'auwa a tsakanin mutane da rayuwar muhalli da al'adu, musanman ta wurin kula da talakawa.

 girma take yi ta wurin aiki da shaidar Kiristi kusurwa na masu yada bishara. Sa’alin da suka shiga kowace kusurwa na Duniya, ya kamata almajiran Yesu su kasance da kauna ba iyaka, irin kaunar da Ubangiji yak e yi wa dukan mutane. Muna shelar mafificiyar kyau da kyauta da ya bamu: ran sa da kaunar sa.

Dukan mutane da al'adu suna da dama su karbi sako na ceto wanda kyauta ne ga kowa. Idan muka dubi rashin adalci, yake-yake da halin takaici da ke fuskantar mutane da har yanzu baa cimma magancewa ba zamu gani cewa dole ne a kai wannan sako na ceto ga kowa. Masu kai bishara sun sani cewa bishara ta yafewa da jinkai na iya kawo sulhuntawa, adalci da salama. Umurnin Ubangiji cikin Bishara "Don haka sai ku je ku almajirantar da dukkan al'ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Da, da Ruhu Mai Tsarki, kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umurce ku" (Matiyu 28:19-20) bai katse ba; umurnin yana kiran mu ne duka, bisa ga yanayin kasashen mu da kalubale da dama, mu ji kira da sabuwar "nishin rai" na bishara kamar yadda na jaddada a kalachen karfafawa ta Manzanci na Evangelii Gaudium: "Kowane Kirista da kowace muhalli dole ne a gane hanyar da Ubangiji ya nuna, amma dukanmu an bukaci biyayya ga kiransa daga garemu mu bar wurin anashuwar mu domin mu je mu kai bishara ga wurare masu nisa da ake bukatar hasken Bisharar" (20).

Wannan shekara ta babban buki ta cika shekaru 90 na kafa ranan duniya ta Bishara (World Missionary Day) wanda Papa Roma Pius XI ya fara bada yarda a yi a shekara ta 1926 sannan Kungiya domin yada Bangaskiya daga offshin Papa Roma (Pontifical Society for the Propagation of the Faith) ta shirya ta kuma aiwatar. Dadai ne in tuna da umarnin wadanda na gada cewa wannan kungiya ta karbi dukan baiko na kowane Diosis, Parish, Kungiyoyin Addini kungiyoyi na chochi chochi a duniya baki daya domin kula da muhallai na Kirista da ke cikin bukata, da kuma ba ma aikin yada bishara tallafi har zuwa karshen duniya. A yau kuma mun yarda da wannan alama ta zumuntan Ikkilisiya. Kada mu kulle zukatan mu cikin namu damuwoyi amma mu bude su don bil'adama gaba daya ta sami suhuwa ta wurin mu.

Bari Mariya Mai Tsarki, mafiya daraja ga ceton bil’adama, makoyiyar masu yada bishara na Ikkilisiya, ta koya wa dukan maza, mata da iyalai domin su inganta su kuma kyautata a ko ina, kasancewar Ubangiji wanda ya tashi daga matattu. Shi wanda yake sabunta dangantaka tsakanin mutane, al’adu da mutane gaba daya, wanda yana cika kowa da Jinkai mai dadi.

Daga Vatikan, 15 Mayu 2016, Idin Fentikos

PAPAROMA FRANCIS

 

English Translation

Missionary Church, Witness of Mercy

 

Dear Brothers and Sisters,

The Extraordinary Jubilee of Mercy, which the Church is celebrating, casts a distinct light on World Mission Sunday 2016: it invites us to consider the missio ad gentes as a great, immense work of mercy, both spiritual and material. On this World Mission Sunday, all of us are invited to "go out" as missionary disciples, each generously offering their talents, creativity, wisdom and experience in order to bring the message of God’s tenderness and compassion to the entire human family. By virtue of the missionary mandate, the Church cares for those who do not know the Gospel, because she wants everyone to be saved and to experience the Lord’s love. She “is commissioned to announce the mercy of God, the beating heart of the Gospel” (Misericordiae Vultus, 12) and to proclaim mercy in every corner of the world, reaching every person, young or old.

When mercy encounters a person, it brings deep joy to the Father’s heart; for from the beginning the Father has lovingly turned towards the most vulnerable, because his greatness and power are revealed precisely in his capacity to identify with the young, the marginalized and the oppressed (cf. Deut 4:31; Ps 86:15; 103:8; 111:4). He is a kind, caring and faithful God who is close to those in need, especially the poor; he involves himself tenderly in human reality just as a father and mother do in the lives of their children (cf. Jer 31:20). When speaking of the womb, the Bible uses the word that signifies mercy: therefore it refers to the love of a mother for her children, whom she will always love, in every circumstance and regardless of what happens, because they are the fruit of her womb. This is also an essential aspect of the love that God has for all his children, whom he created and whom he wants to raise and educate; in the face of their weaknesses and infidelity, his heart is overcome with compassion (cf. Hos 11:8). He is merciful towards all; his love is for all people and his compassion extends to all creatures (cf. Ps 144:8-9).

Mercy finds its most noble and complete expression in the Incarnate Word. Jesus reveals the face of the Father who is rich in mercy; he “speaks of [mercy] and explains it by the use of comparisons and parables, but above all he himself makes it incarnate and personifies it” (John Paul II, Dives in Misericordia, 2). When we welcome and follow Jesus by means of the Gospel and sacraments, we can, with the help of the Holy Spirit, become merciful as our heavenly Father is merciful; we can learn to love as he loves us and make of our lives a free gift, a sign of his goodness (cf. Misericordiae Vultus, 3). The Church, in the midst of humanity, is first of all the community that lives by the mercy of Christ: she senses his gaze and feels he has chosen her with his merciful love. It is through this love that the Church discovers its mandate, lives it and makes it known to all peoples through a respectful dialogue with every culture and religious belief.

This merciful love, as in the early days of the Church, is witnessed to by many men and women of every age and condition. The considerable and growing presence of women in the missionary world, working alongside their male counterparts, is a significant sign of God’s maternal love. Women, lay and religious, and today even many families, carry out their missionary vocation in various forms: from announcing the Gospel to charitable service. Together with the evangelizing and sacramental work of missionaries, women and families often more adequately understand people's problems and know how to deal with them in an appropriate and, at times, fresh way: in caring for life, with a strong focus on people rather than structures, and by allocating human and spiritual resources towards the building of good relations, harmony, peace, solidarity, dialogue, cooperation and fraternity, both among individuals and in social and cultural life, in particular through care for the poor.

In many places evangelization begins with education, to which missionary work dedicates much time and effort, like the merciful vine-dresser of the Gospel (cf. Lk 13:7-9; Jn 15:1), patiently waiting for fruit after years of slow cultivation; in this way they bring forth a new people able to evangelize, who will take the Gospel to those places where it otherwise would not have been thought possible. The Church can also be defined as "mother" for those who will one day have faith in Christ. I hope, therefore, that the holy people of God will continue to exercise this maternal service of mercy, which helps those who do not yet know the Lord to encounter and love him. Faith is God’s gift and not the result of proselytizing; rather it grows thanks to the faith and charity of evangelizers who witness to Christ. As they travel through the streets of the world, the disciples of Jesus need to have a love without limits, the same measure of love that our Lord has for all people. We proclaim the most beautiful and greatest gifts that he has given us: his life and his love.

All peoples and cultures have the right to receive the message of salvation which is God’s gift to every person.  This is all the more necessary when we consider how many injustices, wars, and humanitarian crises still need resolution. Missionaries know from experience that the Gospel of forgiveness and mercy can bring joy and reconciliation, justice and peace. The mandate of the Gospel to "go therefore and make disciples of all nations, baptizing them in the name of the Father and of the Son and of the Holy Spirit, teaching them to observe all that I have commanded you" (Mt 28:19-20) has not ceased; rather this command commits all of us, in the current landscape with all its challenges, to hear the call to a renewed missionary "impulse", as I noted in my Apostolic Exhortation Evangelii Gaudium: "Each Christian and every community must discern the path that the Lord points out, but all of us are asked to obey his call to go forth from our own comfort zone in order to reach all the ‘peripheries’ in need of the light of the Gospel” (20).

This Jubilee year marks the 90th anniversary of World Missionary Day, first approved by Pope Pius XI in 1926 and organized by the Pontifical Society for the Propagation of the Faith.  It is appropriate then to recall the wise instructions of my Predecessors who ordered that to this Society be destined all the offerings collected in every diocese, parish, religious community, association and ecclesial movement throughout the world for the care of Christian communities in need and for supporting the proclamation of the Gospel even to the ends of the earth.  Today too we believe in this sign of missionary ecclesial communion. Let us not close our hearts within our own particular concerns, but let us open them to all of humanity.

May Holy Mary, sublime icon of redeemed humanity, model of missionaries for the Church, teach all men, women and families, to foster and safeguard the living and mysterious presence of the Risen Lord in every place, he who renews personal relationships, cultures and peoples, and who fills all with joyful mercy.

From the Vatican, 15 May 2016, Solemnity of Pentecost

FRANCIS

Category